1 Nuwamba 2020 - 14:27
​Gwamnatin Yahudawan Isra’ila Sun Rusa Gidajen Falasdinawa 129

Kungiyar kwatar ‘yencin Falasdinawa (PLO) ta bada sanarwan cewa gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) ta rusa gidajen Falasdinawa 129 a cikin wannan shekara ta 2020 da muke ciki kadai.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Spotnik na kasar Rasha ya nakalto hukumar kula da filayen Falasdinawa karkashin kungiyar PLO ta na fadar haka.

Ta kuma kara da cewa wannan adadinin rushe-rushe shi ne mafi muni a tarihin gwamnatin yahudawan .

Labarin ya kara da cewa a shekara ta 2016 ma gwamnatin yahudawan ta rusa gidajen Falasdinawa 123.

Har’ila yau Labarin ya kara da cewa rushe-rushen gidajin Falasdinawa na wannan shekarar ya auku ne mafi yawa a birnin Qudus.

Kuma sun auku ne bayan da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya shelenta “Yarjejeniyar Karni” a cikin watan Jenerun wannan shekara (19).

342/